Bauchi 2027: APM Ta Nemi Kotu Ta Soke Takarar Shehu Buba
Daga Zainab Idris Bamalli | TNL HAUSA
Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) a Jihar Bauchi ta shigar da ƙara a Kotun Tarayya da ke Bauchi, tana ƙalubalantar cancantar Sanata Shehu Buba Umar na jam’iyyar PRP, domin tsayawa takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta nemi kotu ta binciki ko shigarsa zaɓen fitar da gwani na PRP da kuma samun tikitin takara sun dace da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.
Mai ba APM shawarar shari’a, Barista Jidauna Tula, ya bayyana cewa jam’iyyar na zargin cewa sunan Shehu Buba bai cikin rajistar mambobin PRP da aka miƙa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a lokacin da doka ta tanada ba. Haka kuma, ta yi zargin cewa ya kasance mamba a APC bayan miƙa rajistar.
APM ta nemi kotu ta soke takarar Shehu Buba tare da umartar INEC ta cire sunansa daga jerin ‘yan takarar gwamnan Bauchi na 2027 idan aka tabbatar da cewa an karya doka.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, INEC, PRP da Sanata Shehu Buba Umar ba su mayar da martani kan ƙarar ba.
TNL HAUSA
Fassara: Zainab Idris Bamalli


No comments