Ali Nuhu Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
Daga Hadi Bawa
Fitaccen jarumin Kannywood kuma Daraktan Gudanarwa na Hukumar Fina-Finan Najeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, ya tsallake rijiya da baya bayan wani hatsarin mota da aka ruwaito ya rutsa da shi a Abuja.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa, hatsarin ya faru ne a yankin Wuse 2 da ke Abuja, inda motar Ali Nuhu da wasu motoci biyu suka yi karo da juna a tsakiyar hanya.
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Ali Nuhu a wurin da hatsarin ya faru, yayin da yake magana cikin yanayin damuwa tare da wasu mutane da suka taru a wurin.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Hukumar Fina-Finan Najeriya da ta tabbatar da cikakken bayani kan hatsarin ko halin da Ali Nuhu yake ciki bayan faruwar lamarin.
Hatsarin ya sake janyo hankalin jama'a ne saboda ya zo a daidai lokacin da ake sake yaÉ—a wasu bayanai da suka shafi lafiyar fitaccen jarumin a kafafen sada zumunta.
A ranar 19 ga Agusta, 2025, Hukumar Fina-Finan Najeriya ta taɓa ƙaryata wata jita-jitar mutuwar Ali Nuhu da ta yaɗu a kafafen sada zumunta.
A wancan lokacin, hukumar ta bayyana cewa rahotannin ƙarya ne, tare da tabbatar da cewa Ali Nuhu yana raye kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin kwanciyar hankali.
Jita-jitar ta samo asali ne daga wani bidiyo da wani mai amfani da Facebook mai suna Ifeoma Chigbo ya wallafa, wanda ke iƙirarin cewa Ali Nuhu ya rasu. Daga bisani kuma aka yaɗa wani saƙo da ke cewa jarumin ya mutu ne sakamakon hatsarin mota.
Sai dai Daraktan Hulɗa da Jama'a na NFC, Brian Etuk, ya bayyana a wancan lokacin cewa rahotannin ba su da tushe, tare da gargaɗin waɗanda ke yaɗa bayanan ƙaryar.
A wannan karon kuma, har zuwa lokacin da ake haÉ—a wannan rahoton, NFC ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatarwa ko musanta rahoton hatsarin da aka ce ya rutsa da Ali Nuhu a Abuja ba.
Duk ƙoƙarin da Wakilinmu ya yi na jin ta bakin Ali Nuhu ko wani daga cikin waɗanda ke kusa da shi domin samun ƙarin bayani kan halin da yake ciki bai yi nasara ba.


No comments