Breaking News

2027: Kano Na Cikin Jihohin Da Za Su Iya Zama Ƙalubale Ga Tinubu


Daga Zainab Idris Bamalli, TNL Hausa

Yayin da zaɓen shugaban ƙasar na 2027 ke ƙara kusantowa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya fuskantar ƙalubalen siyasa a wasu jihohi, sakamakon matsin tattalin arziki, rashin tsaro da kuma tasirin 'yan adawa.

Wani rahoto na Cibiyar Nazarin Zaɓe ta International Republican Institute (IRI) ya bayyana cewa waɗannan matsaloli na daga cikin abubuwan da za su iya tasiri ga zaɓen mai zuwa.

A jihar Kano, tasirin tsohon gwamna kuma ɗan siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na daga cikin abubuwan da ake ganin za su taka rawa a siyasar jihar.

Masanin harkokin siyasa, Farfesa Abubakar Kari, ya bayyana cewa Kano na da tarihin goyon bayan 'yan takarar jam'iyyun adawa a zaɓen shugaban ƙasa.

A zaɓen 2023, Kwankwaso ya samu ƙuri'u 953,179 a Kano, yayin da Tinubu ya samu ƙuri'u 513,846.

TNL Hausa

No comments