'Yan Sanda Sun Cafke Wadda Ta Jefa Opay Cikin Rudani
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta kama wata matashiya mai suna, Hafsat Abubakar, mai shekaru 27, bisa zargin ƙirƙira da yaɗa wata takardar bogi da ke cewa kamfanin OPay zai daina aiki.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa Jami’in hulÉ—a da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, ya bayyana cewa an kama Hafsat a ranar 4 ga Satumba 2026, sa'adda OPay ta kai Æ™orafi ga rundunar a ranar 31 ga Agusta.
Ya ce cibiyar yaÆ™i da laifukan yanar gizo ta ‘yansanda ta gudanar da binciken Æ™waƙƙwafi na Internet, inda aka gano cewa takardar ta samo asali ne daga wani shafin X da Hafsat Abubakar ke amfani da shi.
‘Yan sandan sun ce takardar ta bogi ce kuma an gabatar da ita tamkar sanarwar hukuma daga OPay, inda ta yi ikirarin cewa kamfanin zai dakatar da ayyukansa daga 1 ga Satumba.
OPay ya musanta sanarwar, yana mai cewa kamfanin na ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Rundunar ‘yansandan ta yi gargadin cewa yaÉ—a bayanan bogi ta kafafen sada zumunta na iya haifar da firgici, matsalar kuÉ—i da kuma É“ata sunan kamfanoni.
Ta kuma buÆ™aci jama’a da su riÆ™a tabbatar da sahihancin muhimman bayanai daga majiyoyin hukuma kafin su yaÉ—a su.


No comments