Breaking News

Ya Kamata Opay Ta Gaggauta Sakin Hafsah - Bashir Ahmad

Daga Asma'u Bello, Zaria

A daidai lokacin da rigimar kamfanin Opay da matashiya Hafsat Abubakar ke ƙara yin ƙamari, yayin da hukumar 'yan sanda ta cika hannunta da matashiyar, kwatsam Mallam Bashir Ahmad, Hadimin Marigayi Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya buƙaci Opay, da ta gaggauta sakin Matashiyar, da ta kama bayan zargin karyar cewa za a rufe kamfanin a Najeriya.

TNL HAUSA ta ruwaito cewar, tsohon hadimin shugaban ƙasar  ya roƙi kamfanin na OPay Digital Services Limited, da ya sake duba batun kama Hafsah Abubakar.
Ahmad ya ce matashiyar ta amince cewa abin da ta yi kuskure ne, sannan ta goge saƙon, tare da ba da haƙuri, kamar yadda kamfanin na OPay ya buƙata.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon hadimin ya ce ya fahimci cewa OPay ta buƙaci matashiyar ta cire saƙon tare da neman afuwa cikin wani lokaci da aka kayyade, kuma ta yi hakan.

Shin me za ku ce?

No comments