Wata Mata Ta Mutu Bayan An Mata Gyaran Jiki Sau Shida Lokaci Guda
Daga Asma'u Bashir Bello, Kaduna
Wata mata mai shekaru 51, Andreia Vieira Gaspar, ta mutu a Brazil bayan da ta yi aikin gyaran jiki guda shida a lokaci É—aya cikin wata tiyata da ta dauki tsawon sa’o’i takwas.
Andreia, wadda ke zaune a Spain, ta shafe shekaru biyu tana tara kuÉ—i har ta kai Brazilian Real 118,000, kimanin dala 22,918, domin gudanar da ayyukan, ciki har da gyaran fuska, fatar ido, cire kitsen jiki da kuma dasa kitse a fuska.
Rahotanni sun ce ta mutu ne a ranar 12 ga Agusta, kwanaki bayan kammala aikin a wani asibiti da ke Goiânia.
’Yar uwarta, Djiane Vieira, ta nemi a binciki mutuwar, tana zargin cewa ba a gudanar da cikakkiyar duba lafiyarta kafin aikin a Brazil ba.
Ta kuma ce harshen Andreia ya kumbura sosai bayan tiyatar, kuma duk da Æ™oÆ™arin tuntuÉ“ar jami’an lafiya, ta yi ba ta samu kulawar da ta dace ba. Ta yi zargin cewa asibitin ba shi da sashen kula da marasa lafiya masu tsanani (ICU) ko motar É—aukar marasa lafiya ta gaggawa.
A cewar Djiane, Andreia ta rasu a hannunta bayan ma’aikatan lafiya sun yi Æ™oÆ™arin farfaÉ—o da ita.
Likitan da ya shiga aikin, Lessandro Martins, ya ƙi yin bayani kan yanayin lafiyar marigayiyar, yana mai cewa dokar sirrin likitanci ta hana bayyana bayanan mara lafiya.
Lauyan asibitin ya ce an ba Andreia kulawar gaggawa nan take bayan samun matsala, tare da É—aukar matakan da suka dace.
Hukumomin da abin ya shafa na shirin gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta.



No comments