Breaking News

Rundunar 'Yansandan Jihar Bauchi Ta Yi Wawan Kamu




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Gambo Hassan, mai shekaru 53, wanda yayi kaurin suna wajen yin garkuwa da mata yana kaisu wani guri yayi musi fyade


An kama shi ne a ranar 11 ga Satumba, 2026, a layin Adamu Jumba Road, yana tuka babur kirar Bajaj mai lamba BAU 150G, sanye da abin rufe fuska da hula, tare da wata wuka mai kaifi da yake amfani da ita wajen razana mata


A yayin bincike, wanda ake zargin ya taimaka wajen gano mata 35 da ake zargin sun kasance wadanda ya aikata wa laifukan fyade


Binciken gidansa ya kuma haifar da kwato:

📱 Wayoyi 15

🔋 Power Bank 3

⌚ Agogon mata 6

🧢 Huluna 6

🧕 Hijabai 3

👗 Zannuwan mata 5

💰 ₦425,435, da kuxin Kenya da Turkiyya, da wasu kayayyaki


An tura wanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato zuwa State CID Bauchi domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu

No comments