Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Bai Wa Hafiza Maryam Kyautar N20m
Daga Wakilinmu
Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa Hafiza Maryam Ibrahim Ɗan Azumi kyautar kuɗi har naira miliyan 20, bisa nasarar da ta samu a gasar Musabaƙar Alƙur’ani ta Duniya.
TNL HAUSA ta ba da rahoton cewa, Hafiza Maryam, wadda ta fito daga Jihar Gombe, ta zo ta ɗaya a gasar Musabaƙar Alƙur’ani ta Duniya da aka gudanar a Saudiyya da aka gudanar a watan da ya gabata, inda ta wakilci Najeriya tare da samun gagarumar nasara.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta yaba wa Hafiza Maryam tare da bayyana farin cikinta kan wannan nasara da ta samu, tana mai cewa abin alfahari ne ga Najeriya da kuma al’ummar jihar Gombe.
An ba Hafiza Maryam kyautar kuɗin ne a yayin da Gwamnan Jihar Gombe, Malam Inuwa Yahaya, ya gabatar da ita ga Uwargidan Shugaban Ƙasar domin taya ta murnar wannan gagarumar nasara da ta samu a gasar ta duniya.
Sanata Oluremi Tinubu ta kuma jinjina wa Hafiza Maryam bisa ƙoƙarinta da ƙwarewarta wajen karatun Alƙur’ani, tare da bayyana fatanta cewa nasarar za ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga sauran matasa masu karatun Alƙur’ani a Najeriya.
Nasarar Hafiza Maryam ta ƙara ɗaukaka sunan Najeriya da jihar Gombe a fagen gasar karatun Alƙur’ani ta duniya, tare da nuna irin ƙwarewar da matasan ƙasar ke da ita a fannin karatun Alƙur’ani.
Kyautar Naira miliyan 20 da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bai wa Hafiza Maryam na daga cikin abubuwan da suka ƙara haskaka muhimmancin nasarar tata, tare da ƙarfafa mata gwiwa wajen ci gaba da neman ilimi da bunƙasa ƙwarewarta a karatun Alƙur’ani.


No comments