Abin Da Ya Sa Na Yi Watsi Da Muƙamin Da Aka Ba Ni A Kwamitin Neman Sake Zaɓar Tinubu -Jarumar Nollywood
Daga Hadi Bawa
Fitacciyar jarumar Nollywood, Toyin Abraham, ta yi bayanin dalilin da ya sa ta ƙi amincewa da kasancewarta cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a jihar Legas, inda ta ce an saka sunanta cikin jerin sunayen kwamitin ba tare da saninta ba, kuma ba ta da sha’awar shiga harkokin siyasa
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026, yayin da take mayar da martani ga wani mai amfani da kafar sada zumunta da ya yi zargin cewa matakin nata na iya hana wasu mutane ci gaba da suka da cin zarafi a kafafen sada zumunta, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai Toyin ta ce ba saboda irin wannan suka ko cin zarafi ta ɗauki matakin ba, tana mai cewa ta yi hakan ne saboda ta ga hakan shi ne abin da ya dace.
Ta ce ta farka ne ta ga sunanta cikin jerin sunayen kwamitin, alhali ba ta san komai game da batun ba.
Ta kuma jaddada cewa tun da farko ta bayyana matsayarta na cewa ba ta da sha’awar shiga siyasa. “Na riga na faɗa cewa ba na sha’awar siyasa,” in ji Jarumar.
Tun da farko, Toyin ta nisanta kanta da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na Legas, bayan da sunanta ya bayyana cikin jerin mambobin sashen nishaɗantarwa.
Ta buƙaci jama’a su yi watsi da rahotannin da ke cewa tana cikin kwamitin, tana mai cewa ba ta cikin wani kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu.
TNL HAUSA ta fahimci cewa sunan Toyin ya bayyana tare da na wasu fitattun ‘yan fim da masu nishaɗantarwa ciki har da Jide Kosoko, Eniola Badmus, Bimbo Akintola, Adebayo Salami, Saheed Balogun da Bukky Wright.
Takardar kwamitin ta nuna cewa Toke Benson-Awoyinka ce ke jagorantar sashen, yayin da Jide Kosoko yake mata mataimaki, Eniola Badmus kuma mataimakiyar darakta.
Matakin na Toyin ya zo ne shekaru uku bayan da ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lamarin da ya jawo mata suka da cece-kuce a kafafen sada zumunta.
A halin yanzu dai, duk da ƙin amincewarta, sunanta yana nan a cikin takardar da aka wallafa ta kwamitin, a matsayin ɗaya daga cikin mambobin sashen mai mutum 33.
Abin da jama'a ke mamaki shi ne yadda wannan Jarumar ta nisanta kanta wannan muƙamin da ta samu, yayin da wasu ke hasashen anya za a samu wata 'yar Kannywood ta samu wannan damar ta bar ta kuwa?


No comments