Breaking News

Sanata La’ah Zai Yiwa NDC Takarar Gwamna A Kaduna


Jam’iyyar National Democratic Congress, NDC, ta ayyana Sanata Danjuma Tella La’ah a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Kaduna da ta gudanar.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani, Dakta Danlami Arab, ne ya bayyana sakamakon a ƙarshen zaɓen da aka gudanar a Kaduna.

Ya ce Sanata Danjuma La’ah ya samu ƙuri’u dubu shida da ɗari tara da casa’in, yayin da wanda ya zo na biyu, Barista Sani Abbas, ya samu ƙuri’u ɗari huɗu da biyu.

Dakta Arab ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana, kuma bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

A jawabinsa na godiya bayan nasarar, Sanata Danjuma La’ah ya gode wa magoya bayan jam’iyyar bisa amincewa da shi ya yi wa jam’iyyar takara a babban zaɓen shekarar 2027.
Ya kuma yi alkawarin cewa zai yi aiki tuƙuru domin kawo sauyi da ci gaba a jihar Kaduna idan aka zaɓe shi.

No comments