Rikicin makamashi: Kwararre kan makamashi ya bukaci gwamnati ta rungumi wutar hasken rana
Daga Najeeb Sani, Bauchi
Kwararre kan makamashin hasken rana, Engr. Abubakar Yusha’u Adamu, ya ba da shawarar cewa gwamnatocin jihohin arewa da gwamnatin tarayya su rungumi amfani da wutar hasken rana da iska a matsayin hanyoyin da za su magance matsalar rashin wutar lantarki da kasar ke fama da ita.
Adamu wanda ya zanta da wakilin mu a garin Futuk, karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, inda yake kula da aikin samar da wutar hasken rana ga dukan al’ummar yankin, ya ce wutar hasken rana “ta fi dacewa da dogaro fiye da na’urar wutar lantarki ta kasa wadda ta dogara da wutar ruwa.”
“Muna ba gwamnati shawara, musamman a arewa nan, ta duba yiwuwar amfani da wutar hasken rana ko iska a matsayin madadin wutar ruwa ta na’urar wutar lantarki ta kasa.
"Suna da dogaro cikin kashi dari bisa dari, sun fi na’urar wutar lantarki ta kasa wadda ta dogara da wutar ruwa dogaro,” in ji shi.
Kwararren ya ce ana amfani da wutar hasken rana a jihar Bauchi a halin yanzu, inda ya bayyana dajin Yankari a matsayin misali, wacce yanzu haka wutar hasken rana ita ce babbar hanyar samar da wutar lantarki a can.
Ya bukaci gwamnati ta rungumi wannan hanyar domin bunkasa harkokin kasuwanci.
Ya bayyana wutar lantarki a matsayin “tushen rayuwar kowace kasuwanci” kuma ya ce wutar hasken rana dabara ce, mai sabuntawa kuma mai sauki da arha.
A cewarsa, idan aka yi amfani da wutar hasken rana yadda ya kamata, za ta iya ba da wutar lantarki ba tare da katsewa ba.
Engr. Adamu ya kara bayyana cewa har ma fadar shugaban kasa tana sauya sheka zuwa wutar hasken rana, yana mai jaddada cewa idan cibiyar gwamnati za ta iya rungumarta, to sauran sassan kasar ma su bi sahun.
“Idan gidan shugaban kasa za ta zabe ta, me ya sa ba dukan kasa ba, tunda ba mu iya magance matsalar wutar ruwa ta mu tsawon shekaru ba?,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnatocin jihohin arewa da su saka kudi wajen samar da wutar hasken rana da iska domin bunkasa samun wutar lantarki, tallafa wa kasuwanci da kuma rage dogaro da “na’urar wutar lantarki ta kasa wadda bata da tabbas.”


No comments