Gwamna Uba Sani ya yi Rabon motoci a kaduna.
Daga Abdullahi Sambo Richifa
Kungiyoyi da ma'aikatu da dama sun Sami tallafin motoci daga wajen Gwamnar jihar Kaduna Malam Uba Sani.
Ma'aikatu da kungiyoyin da suka Sami wannan tallafin motocin dai sun hada da Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Ƙungiyar ’Yan Jarida (NUJ), Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) da kuma Hukumar Gyaran Hali.
Sabbin motocin haya dai an ba su ne domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri da zirga-zirga a al'amuran su na yau da kullun.
Gwamnan ya ce ƙungiyoyi da hukumomin na daga cikin muhimman masu ruwa da tsaki da ke taka rawa wajen ci gaban Jihar Kaduna.
Da yake karɓar motar a madadin ’yan jarida, Shugaban NUJ na Kaduna, AbdulGafar Alabelewe, ya ce ƙungiyar ta nemi tallafin motar ne kimanin watanni shida da suka gabata, a lokacin wata liyafar Ramadan da Gwamna Uba Sani ya halarta.
Alabelewe ya ce NUJ Kaduna ba ta samu irin wannan tallafi daga gwamnatin jihar ba tsawon kusan shekaru 20, yayin da tsohuwar motar ƙungiyar ta daina aiki. Ya ce sabuwar motar za ta taimaka wa ’yan jarida wajen gudanar da ayyukansu da zirga-zirga zuwa sassan jihar.
Shi ma Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Kaduna , wato KASU, Prof. Abdullahi Musa, ya bayyana tallafin a matsayin wani muhimmin tarihi ga jami’ar, tare da yabawa Gwamna Uba Sani bisa karamci da kulawarsa a gare su. Ya ce wannan zai saukaka musu sosai a bangaren zirga-zirga a makarantar.


No comments