Breaking News

Ko Hisbah Za Ta Iya Kawo Ƙarshen Baɗala A Kano?

Daga Hadi Bawa 

 A wannan makon ne, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane 22 da ake zargin suna kwaikwayon shiga ta yanayin jinsi na kishiyantar jinsunsu bayan samun korafe-korafe daga mazauna jihar.

Mataimakin Kwamandan Janar na Hukumar, Dr. Mujahid Aminuddeen ne ya tabbatar da kama mutanen, inda ya ce an cafke su ne a yankunan Zoo Road, Court Road da wasu wuraren da ke maƙwabtaka da su.

Ya ce mafi yawancin mutanen da aka kama sun shigo Kano ne daga wasu jihohin ƙasar.

A cewarsa, waɗanda aka kama sun ƙunshi mata 10 da maza 12, kuma sun amsa cewa suna gudanar da harkokin haɗuwa domin yin lalata, tare da shan miyagun ƙwayoyi.

Sai dai har yanzu rubuta wannan rahoton TNL Hausa ba ta samu jin ta bakin ɓangaren da aka kama ba, yayin da Hukumar Hisba ta bayyana cewa za ta gurfanar da su a gaban kotu.

Hukumar Hisba ta sha alwashin kawo karshen baɗala a duk faɗin jihar Kano.

Za ta iya kuwa?

No comments