Breaking News

JKD TV Ta Karyata Batun Kama Ma’aikatanta Kan Bidiyon Ibrahim Masari

Daga Al-Amin Ciroma

Gidan talabijin na JKD TV da ke Kaduna ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kama Shugabar Shirye-shiryen tashar, Zainab Salihu Yabagi, da wasu jami’an tsaron tashar, biyo bayan wata taƙaddama da ta shafi wani bidiyo da aka wallafa a shafin tashar, a kafafen sada zumunta.

Tashar ta tabbatar da cewa jami’an ’yan sanda sun ziyarci harabarta ne bisa wata ƙorafi da ake zargin tawagar Ibrahim Kabir Masari, mai ba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa da ayyukan musamman, ta shigar.

A cewar bayanan da TNL HAUSA ta samu kai tsaye, ƙorafin ya biyo bayan wallafa wani bidiyo da tawagar Masari ta ce yana ƙunshelile da kalaman da za su iya zubar da mutuncinsa.

Sai dai TNL HAUSA ta tattaro cewa yanayin da ziyarar ’yan sandan ta gudana, ya sha bamban matuƙa da yadda wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo suka ruwaito lamarin.

Mista Charles J. Abbah, wanda aka fi sani da Engr. Random, kuma shugaban JKD TV Kaduna, ya ce tun farko ’yan sandan sun nemi kama Zainab Salihu Yabagi ne bisa zargin cewa ita ce ta wallafa bidiyon da ake taƙaddama kansa.

Sai dai Abbah ya ƙalubalanci dalilin kamun nata kan abin da aka wallafa ta shafin kamfani, ba wai a na ta ba.

Injiniya Random ya shaida wa wakilinmu cewa Yabagi tana gudanar da aikinta ne, kuma ta wallafa bidiyon ne a shafin kamfanin, ba ta shafinta na ƙashin kanta ba.

Daga bisani, Abbah ya miƙa kansa ga ’yan sanda tare da amsa gayyatar da aka yi masa zuwa rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, inda ya gana da Kwamishinan ’Yan Sanda da kuma Kakakin Rundunar ’Yan Sanda.

A cewarsa, ya shafe wasu sa’o’i a rundunar yana tattaunawa da jami’an ’yan sanda kan lamarin, kafin ɓangarorin biyu suka amince da sake zama a ranar Litinin, 14 ga Satumba, domin ƙarin bayani da fayyace sauran batutuwan.

“Ba kama kowa ba  gaskiya, domin na je ne na amsa tambayoyi, kuma mun bayyana matsayinmu ƙarara. Da farko sun so su kama Zainab Salihu Yabagi, wadda ita ce Shugabar Shirye-shiryenmu, amma na sanar da su cewa ita ta yi aikinta ne kuma ta wallafa abin a shafin kamfan, ba a shafinta na ƙashin kanta ba,” in ji Abbah.

“Saboda haka, idan suna da matsala da abin da aka wallafa, za su iya kai ƙarar kamfani, ba mutum Zainab ba. Don haka, ba a kama ta ba, kuma ba a gayyace ta ba. Mun tattauna, sannan muka ɗage batun zuwa ranar Litinin, 14 ga Satumba, domin ƙarin bayani. A yanzu haka, ina gidana cikin kwanciyar hankali.”

Abbah ya kuma bayyana cewa ’yan sandan sun gayyaci wani jami’in tsaro da ke aiki a tashar talabijin ɗin, bisa zargin cewa jami’in ya nuna rashin ladabi ko girman kai ga jami’an ’yan sandan a lokacin da suka kai ziyara tashar.

Sannan, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa an kai samame a tashar tare da kama wasu daga cikin ma’aikatanta.

Wannan bayani ya sauya yadda ake kallon rahotannin farko da suka bayyana lamarin a matsayin samamen ’yan sanda da ya kai ga kama wasu ma’aikatan JKD TV.

Duk da cewa har yanzu ba a warware takaddamar ba, bayanai na cewa ’yan sanda na duba ƙorafin ne ya zuwa yanzu.

Abbah ya kuma bayyana cewa ƙungiyar Amnesty International na bibiyar abubuwan da ke faruwa dangane da lamarin, kuma a shirye take ta shiga tsakani idan al’amuran suka tsananta ko kuma suka haifar da damuwa kan haƙƙin tashar ko ma’aikatanta.

No comments