Breaking News

Gombe: Tsohuwar Shugabar Matan PDP Da Tsohuwar Kwamishina, Sun Koma APC

Daga Najeeb Sani 

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Gombe ta karɓi manyan jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki.

Wadanda suka sauya shekar sun hada da Hajiya Hannatu Wakil, wacce ta yi aiki a matsayin Shugabar Matan PDP na Jiha tsawon shekaru takwas sannan ta zama Sakataren Tsare-Tsare na Jiha, da tsohuwar Kwamishina Hajiya Asabe Baba Nahaya, da tsohon Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman, Hon. Sarki Alban, da kuma Hon. Yila Y. Mustafa, wanda ya tsaya takarar kujerar Dan Majalisar Tarayya na Balanga/Billiri a karkashin jam'iyyar PDP a zabukan 2011 da 2015.

Sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar gwamnan APC a jihar a zaben 2027, Dr. Jamilu Isyaku Gwamna.

Bangaren Gwamna ya marabci wadanda suka sauya shekar, inda ya bayyana matakin a matsayin wani babban ci gaba ga APC da kuma karin tabbatar da karuwar amincewar jama'a ga burin Dr. Gwamna na jagorantar Jihar Gombe a 2027.
Za a iya tunawa cewa kwanan nan, tsohon ma'ajin jam'iyyar PDP na kasa, Hon. Ahmed Yayari, ya fice daga jam'iyyar ya kuma shiga tawagar yakin neman zaben Gwamna.

No comments