Breaking News

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji Na Neman 'Gentle De Yahoo' Ruwa A-jallo, Tare Da Sanya Kyautar Naira Miliyan 30 Kansa

Daga Al-Amin Ciroma 

Rundunar sojin Najeriya ta ayyana Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da 'Gentle De Yahoo,' a matsayin wanda ake nema ruwa a-jallo, tare da sanya kyautar Naira miliyan 30 ga duk wanda ya bayar da sahihin bayanin da zai kai ga cafke shi.

Sanarwar ta fito ne daga Rundunar Hadin Gwiwa ta Sojin Kudu maso Gabas, wato Operation UDO KA, wadda ta bayyana Okorienta a matsayin barazana ga zaman lafiya a yankin.

A cikin sanarwar da aka fitar ranar Lahasi, kamar yadda TNL HAUSA ta ruwaito, rundunar ta buƙaci jama’a da ke da sahihin bayani kan inda 'Gentle De Yahoo' yake da su tuntuɓi hukumomin tsaro kai-tsaye.

Rundunar ta bayar da lambobin waya kamar haka: 193 da 08067959570, domin isar da bayanan, tare da gargaɗin jama’a da kada su yi ƙoƙarin tunkarar wanda ake nema da kansu, ba tare taimakon jami'an tsaro ba.

No comments