Breaking News

Cibiyar CSAI Ta Ƙaryata Zargin Alaƙanta Babban Hafsan Tsaron Najeriya da Siyasa

Daga Al-Amin Ciroma

Cibiyar Nazarin Dabarun Tsaro da Samar da Musamman Bayanai ta CSAI, ta yi watsi da iƙirarin da ke cewa Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, na da hannu cikin harkokin siyasa, ko kuma wata dabarar nuna goyon baya ga wani ɓangare na siyasa.

TNL HAUSA ta ruwaito cewa, cibiyar ta bayyana zarge-zargen a matsayin surutai ne marasa tushe, waɗanda aka ƙago su domin yaudarar jama’a. Haka kuma cibiyar ta CSAI ta yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da duk wasu bayanai ko kalamai da ka iya haddasa ruɗani ko tasgaro ga al'umma kan abubuwan da suka shafi harkar rundunar tsaron Najeriya.

Wannan cece-ku-ce dai, kamar yadda Wakilinmu ya naƙalto, ya samo asali ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi, gabanin babban zaɓen 2027, inda ake ƙara samun hasashe a cikin al’umma kan zargin cewa wasu manyan jami’an tsaro na iya kasancewa da hannu cikin harkokin siyasar.

Har ila yau, CSAI ta jaddada cewa ƙoƙarin danganta Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Oluyede da siyasar ɓangaranci ba shi da wani ingantaccen tushe, kuma bai kamata a bari irin waɗannan zarge-zarge su dauke hankalin shugabannin soji daga sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mu su ba.

Janar Oluyede, kamar yadda TNL HAUSA ta tattara, shi ke jagorantar rundunonin tsaron ƙasar, ya na kuma ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan tsaron ƙasar, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki wajen shugabancin rundunar Sojin Najeriya, musamman yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran barazanar tsaro da ke addabar ƙasar.

A cikin mahimman kalaman da shugabannin soji suka yi a baya-bayan nan, kamar yadda Wakilinmu ya ruwaito, an jaddada muhimmancin tsaron ƙasa, jin daɗi da walwalar jami’an soji da kuma ci gaba da matsin-lamba ga dukkanin gungun ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ’yan ta’adda.

A wannan yanayi ne CSAI ta yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su kasance masu taka-tsantsan wajen gudun yaɗa zarge-zargen da suka shafi manyan jami’an soji, musamman zarge-zargen da ka iya haifar da tashin hankali ko kuma haifar da shakku ga 'yan Najeriya ga hukumomin tsaron ƙasa.

A halin yanzu, saƙon na cibiyar CSAI a bayyane yake, cewar CSAI ta tabbatar dukkanin zarge-zargen da ake dangantawa ga Janar Oluyede kan shiga harkokin siyasa, a matsayin nan ƙanzon-kurege kuma marasa tushe.


No comments