TSOHUWAR AJIYA:Tsohon Shugaba Kasa Gowon, Tare Da Dansa - Ibrahim, Da Ya Yi Wa Sheikh Inyass Takwara
Daga Aliyu Saleh
Wannan muhimmin hoton da aka dauka a shekarar 1975, ya nuna Tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon, a wani titi cikin birnin Landan, tare da ’ya’yansa guda biyu, Ibrahim da Saratu, a lokacin da yake gudun hijira a Birtaniya.
Abin da ya fito da mahimmancin wannan hoton dai shi ne labarin da ke tattare da shi, wato yadda ya rada wa Dansa sunan Ibrahim, kamar yadda TNL HAUSA ta ruwaito.
Janar Gowon ya sanya wa dansa sunan Sheikh Ibrahim Inyass, wato fitaccen malamin addinin Musulunci da yake matukar girmamawa da kauna. Saboda haka, sunan Ibrahim ya kasance wata alama da tsohon shugaban ya yi wa wannan babban malamin addini wanda ya yi tasiri a rayuwarsa.
An dai dauki hoton ne a ranar 25 ga Oktoba, 1975, kamar yadda ake iya gani.


No comments