Yan Sandan Bauchi Sun Tabbatar Da Tsaro A Zaɓen Magoya Bayan Wikki Tourists
Daga Zainab Idris Bamalli TNL HAUSA
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da samar da tsaro yayin zaɓen shugabannin ƙungiyar magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourists, wanda za a gudanar ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026, a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayyana hakan yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan takara 23 suka sanya hannu, inda ya gargaɗe su da su guji tashin hankali, kalaman ƙiyayya da duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya.
Shugaban kwamitin zaɓen, Yahaya Abdulkarim, ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaɓen cikin ’yanci, adalci da gaskiya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ne karon farko tun shekarar 2001 da za a gudanar da zaɓen shugabannin ƙungiyar cikin tsari na zaɓe, maimakon amfani da kwamitin riƙon ƙwarya.


No comments