Breaking News

Ƙungiyar TINUBU Ta bukaci Dan Takaran Gwamna na APC A Bauchi ya yi murabus

Daga Abdullahi Alhassan

Wata ƙungiyar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai suna National Patriotic Front for Tinubu (NPFFT), ta buƙaci ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Mohammed Abubakar, da ya yi murabus daga takararsa gabanin zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ta yi zargin cewa ɗan takarar ba shi da isasshen farin jini da zai iya bai wa APC nasara a jihar.

A cewar ƙungiyar, ya kamata shugabannin APC su sake duba zaɓin ɗan takararsu tare da samar da wanda ya fi samun karɓuwa a wajen al’umma, musamman a matakin ƙasa.

Ta kuma jaddada cewa nasarar zaɓe ba ta dogara da ƙarfin jam’iyya da kuɗi kaɗai ba, sai da goyon bayan masu zaɓe.

Ƙungiyar ta buƙaci Mohammed Abubakar da ya fifita muradun jam’iyyar ta hanyar ajiye takararsa domin bai wa APC damar samun wanda zai iya lashe zaɓen gwamnan Bauchi na 2027.

Fassara by Zainab idris Bamalli

No comments