Breaking News

TUNA BAYA: Tambihi Daga Siyasar Alvan Ikoku Da Ɗansa.

Daga Zainab Bamalli

Wani labari daga tarihin siyasar Najeriya ya bayyana yadda fitaccen malami kuma ɗan kishin ƙasa, Alvan Ikoku, ya nuna haƙuri da mutunta ra’ayin jama’a bayan ɗansa, Samuel Ikoku, ya kayar da shi a zaɓe.

Nazarin ya nuna cewa duk da kasancewarsu uba da ɗa, sun shiga takarar kujerar siyasa ɗaya, amma sakamakon zaɓe bai sa dangantakarsu ta lalace ba.

An bayyana cewa Alvan Ikoku ya amince da sakamakon zaɓen, tare da nuna goyon baya ga makomar siyasar ɗansa.

Wannan lamari na zama darasi ga ’yan siyasa da magoya bayansu a Najeriya, musamman a wannan lokaci da bambancin ra’ayin siyasa kan haifar da saɓani tsakanin abokai, ’yan uwa da maƙwabta.

Darasin shi ne, dimokuraɗiyya tana ba mutane damar zaɓar shugabannin da suke so, amma bai kamata bambancin ra’ayi ya zama sanadin ƙiyayya da rarrabuwar kawuna ba.

Siyasa zabi ce, ba yaƙi ba; kuma bambancin ra’ayi bai kamata ya lalata zumunci da zaman lafiya ba.

No comments