Breaking News

Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Malam Nafiu Baba-Ahmed

Daga Hadi Bawa 

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhinin da juyayin rasuwar Babban Sakataren Majalisar Ƙoli ta Shari’a ta Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed.

Malam Nafiu Baba-Ahmed, wanda ƙwararren Lauya ne, ya kasance fitaccen jagoran addinin Musulunci, ya rasu a safiyar Talata bayan ya kwashe shekaru da dama yana hidima ga addinin Musulunci da ƙasa.

A cikin saƙon ta’aziyyar da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, wacce TNL HAUSA ta samu, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai tasiri, wanda ya jagoranci ayyukan Majalisar cikin hikima, hangen nesa da jajircewa wajen tabbatar da haɗin kai, adalci da zaman lafiya.

Shugaban Ƙasar ya tuna da daɗewar dangantakarsa da Baba-Ahmed, musamman a lokacin shirye-shiryen zaɓen shekarar 2011 da shekarun da suka biyo baya. 

Ya kuma bayyana irin shawarwari da goyon bayan da marigayin ya bayar a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Tinubu ya kuma yaba da rawar da Baba-Ahmed ya taka wajen tabbatar da ci gaba da bayyana matsayar Majalisar kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa, da kuma ƙoƙarinsa na inganta fahimtar juna, farfaɗo da ɗabi’un kirki da tabbatar da adalci a cikin al’umma.

Shugaban Ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban da mambobin Majalisar Ƙoli ta Shari’a ta Najeriya, iyalan Baba-Ahmed, gwamnatin da al’ummar Jihar Kaduna, da kuma ɗaukacin al’ummar Musulmi a Najeriya. 

Ya roƙi Allah ya gafarta wa marigayin kurakuransa, ya ba shi Aljannatul Firdaus, sannan ya ba iyalansa da al’ummar Musulmi ƙarfin jure wannan babban rashi.

No comments