Breaking News

ƘADDAMAR DA YAƘIN NEMAN ZAƁEN TINUBU: Kaduna Ta Tumbatsa, 'Yan Adawa Sun Ragargaji Taron

Zainab Idris Bamalli

Birnin Kaduna ya cika maƙil da magoya bayan jam’iyyar APC da manyan jami’an gwamnati yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi al’umma su sake zaɓensa domin ci gaba da manufofinsa.

Sai dai Jaridar TNL HAUSA ta ruwaito cewa 'yan adawa sun ragargaji sakamakon taron, musamman ma a yayin da Shugaba Tinubu, a cikin jawabinsa da ya ce, 'yan adawa ne suka ƙirkiro matsin tattalin arziƙin da ƙasar ke fuskanta kuma suke sukar gwamnatinsa.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ƙalubalanci wannan iƙirarin da Tinubu ya faɗi, inda ya ce abin kunya ne mutum ya hasa wuta a gidansa, sannan ya ruga maƙwabta yana zarginsu da tayar da hayaƙi.

Atiku ya ce, haƙƙin gwamnati ne ta sauke nauyi da farillun da ke kanta maimakon neman suna wajen ɗora laifin da wasu.

TNL HAUSA ta ruwaito cewa, a wajen taron, Tinubu ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziki da inganta rayuwar matasa, tare da kira ga magoya bayansa da su tabbatar da nasarar APC a dukkan matakan zaɓe.

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya yaba wa gwamnatin tarayya kan ayyukan raya ƙasa da ta gudanar, musamman gyaran hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 123, da aka ce an ware wa aikin naira biliyan 178.

Uba Sani ya kuma bayyana cewa an sake buɗe makarantu sama da 300 da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko fiye da 150 da aka rufe sakamakon matsalar tsaro a jihar.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu, Sanata Abdul’aziz Yari, ya ce an zaɓi Kaduna ne saboda muhimmancinta a siyasar Arewacin Najeriya. Ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da sauran shugabannin al’umma su taimaka wajen wayar da kan jama’a.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada cewa gwamnatin APC na ƙoƙarin bunƙasa ilimi da ababen more rayuwa, tare da inganta haɗin kai tsakanin al’ummomi.

Shettima ya kuma buƙaci ’yan Arewa da su goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027, yana mai cewa ci gaba da manufofin gwamnati na da muhimmanci ga ci gaban ƙasa.

No comments