Tinubu Na Iya Lashe Zaɓen 2027 Duk Da Natsalar Tsaro Da Tsadar Rayuwa -Jaridar The Economist
Daga Aliyu Saleh
Jaridar The Economist da ke Birtaniya ta yi hasashen cewa, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, na iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 duk da rashin gamsuwar da wasu ’yan ƙasa ke nunawa kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da ƙasar.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa, a wani rahoto da jaridar ta wallafa ranar 1 ga Oktoba, ranar bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, ta bayyana matsalar tsaro da ta ƙara tsananta, matsin tattalin arziƙi da sauye-sauyen tattalin arziƙi suka jawo, da kuma kasancewar ’yan takarar adawa masu ƙarfi a matsayin abubuwan da ka iya yin illa ga ƙoƙarin Tinubu na sake komawa kan karaga a karo na biyu.
Sai dai jaridar ta ce kwarin gwiwar Tinubu na komawa na iya kasancewa ne sakamakon yanayin siyasar Najeriya mai sarƙaƙiya, ba wai saboda jama’a sun gamsu da ayyukan gwamnatinsa ba.
Ta ce ’yan takarar da ke kan mulki a Najeriya sun saba samun fa’ida ki tagomashi a zaɓuka saboda damar amfani da tsarin jam’iyya mai mulki da kuma albarkatun da za su iya amfani da su wajen jan hankalin masu zaɓe.
The Economist ta kuma bayyana rarrabuwar kawunan ’yan adawa a matsayin wani abin da zai iya tasiri ga zaɓen.
Ta ce Atiku Abubakar da Peter Obi, waɗanda ke cikin fitattun ’yan adawa, suna takara ne ƙarƙashin jam’iyyun ADC da NDC, kuma rashin haɗa kai a tsakanin su na iya hana ƙuri’un masu adawa da APC haɗuwa wuri guda.
Jaridar ta yi nuni da cewa addini ma na iya taka rawa a zaɓen, musamman a arewacin Najeriya. Ta ce kasancewar Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, Musulmai na iya sa su samu karɓuwa a wasu sassan Arewa, yayin da addinin Peter Obi na Kiristan Katolika ka iya zama wani abin da wasu masu zaɓe za su yi la’akari da shi.
Sai dai ta kuma jaddada cewa ba lallai ne waɗannan abubuwan su bayyana yadda kowane mai zaɓe zai kaɗa ƙuri’arsa ba.
The Economist ta kuma bayyana abin da ta kira “political cynicism”, wato rashin tsammanin cewa zaɓe zai iya kawo sauyi, a matsayin wani abu da ka iya shafar halayyar masu zaɓe.
Jaridar ta ruwaito Joachim MacEbong na Control Risks, yana cewa wasu al’ummomi, musamman a Arewa, sun daɗe suna fuskantar ƙarancin tsaro, kiwon lafiya da ingantattun makarantu, lamarin da ka iya rage irin abubuwan da suke tsammani daga gwamnati.
Ta kawo misalin wata mata a Maiduguri da ta ce za ta zaɓi Tinubu saboda godiya ga maganin da ta samu a wani asibitin gwamnati.
Jaridar ta kuma danganta yanayin zaɓen da yawan mutanen da za su fito su kaɗa ƙuri’a, musamman a wuraren da matsalar tsaro ta yi ƙamari. Ta ce yayin da wasu masu zaɓe za su iya nuna rashin jin daɗinsu da gwamnati, hakan ba lallai ya koma ƙuri’ar adawa da shugaban ƙasa ba.
Ta kuma yi nuni da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba, sannan ci gaban tattalin arziƙin da ake sa ran zai kai kashi 4.1 cikin ɗari a bana bai haifar da sauƙin rayuwa ga jama’a ba, rashin gamsuwa na iya ci gaba, wanda zai iya haifar da rashin tabbas ga makomar Tinubu a zaɓen na 2027.


No comments