Sojojin Sun Ceto Mata 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Daga Hadi Bawa
Sojojin Runduna ta 2 ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto mata biyar da aka yi garkuwa da su, ciki har da wata uwa da jaririnta, yayin wani samame da suka gudanar a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.
Wata majiya daga rundunar sojin ta shaida wa TNL Hausa cewa sojojin sun samu bayanan sirri ne kan motsin ’yan ta’adda a yankin dajin Maɗaci, inda suka yi gaggawar tura dakarunsu domin yi masu ƙofar rago ta hanyar dabarun yaƙi.
Majiyar ta ƙara da cewa, samamen sojojin ya haifar da ruɗani a tsakanin ’yan ta’addan, lamarin da ya ba dakarun damar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su cikin sauƙi.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da wata uwa da jaririnta, da wasu ƙananan yara da matasa uku, waɗanda aka ce sun fito ne daga ƙananan hukumomin Ɗanja da Funtua.
Daga bisani, sojojin sun miƙa waɗanda aka ceto ga shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Musa, domin a sada su da iyalansu.
A halin yanzu, dakarun na ci gaba da gudanar da sintiri mai ƙarfi a yankin, a wani mataki na tabbatar da cikakken iko a dajin da kuma taƙaita zirga-zirgar ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.


No comments