SHEIK ZAKZAKY Yayikira ga Matasa da Su Taka Rawar gani Wajen Yaki da Zalunci
fassara by zainab idris Bamalli
Shugaban Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya bukaci matasa da su yi amfani da karfinsu, iliminsu da damar da suke da su wajen fafutukar tabbatar da adalci da yaki da zalunci.
Zakzaky ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin rufe taron kasa da kasa kan gwagwarmaya da aka gudanar a Abuja, mai taken “Matasa da Makomar Gwagwarmayar Musulunci.”
Malamin ya jaddada cewa matasa su yi amfani da lokacinsu wajen ayyukan alheri da tabbatar da adalci, maimakon jiran tsufa kafin su fara daukar mataki. Ya kuma bukace su da kada su jira bayyanar Imam Mahdi (AS) kafin su tsaya tsayin daka wajen kalubalantar zalunci.
Ya yi nuni da juyin juya halin Musulunci na Iran a matsayin misali na yadda hadin kai, ilimi da jajircewa za su taimaka wajen cimma manufofin da suka shafi adalci.
Haka kuma, Zakzaky ya bukaci matasa Musulmi su mayar da ilimi zuwa aikace-aikace, tare da kiyaye hadin kan al'ummar Musulmi da gujewa tsattsauran ra'ayi da kalaman da ke haddasa gaba da rarrabuwar kai.
Taron ya samu halartar mahalarta daga Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Kamaru da sauran wurare, ciki har da Seyed Hassan Heydari, mai ba da shawara kan al'adu a ofishin jakadancin Iran da ke Abuja.
Karshen Rahoton kenan


No comments