Breaking News

Sabon Hari A Millennium City Ya Sake Jefa Fargaba Ga Jama’ar Kaduna

Daga Al-Amin Ciroma

Al’ummar da ke zaune a rukunin gidajen Nuru Suraj Estate da ke Millennium City a jihar Kaduna, sun shiga cikin firgici bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka kutsa kai unguwar tare da yin awon gaba da mutum shida a safiyar Talata, 27 ga Oktoba, 2026.

TNL Hausa ta ruwaito cewa matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a garuruwa da unguwannin da ke kewaye da Millennium City, lamarin da ya sa mazauna yankin ke cikin fargaba tare da kwana cikin rashin tabbas.

Wannan hari na zuwa ne bayan jerin sace-sacen mutane da aka yi a Millennium City, wata sabuwar ta masu hannu da shuni da ke wajen birnin Kaduna.

Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa maharan sun samu damar shiga cikin unguwar ne ta ƙofa ta biyu, inda suka yi awon gaba da mutanen ba tare da an ci dununsu ba.

Wata mazauniyar yankin mai suna Maman Hamid ita ma ta shaida wa NAN cewa bayan maharan sun kutsa cikin unguwar, sun yi awon gaba da mutanen, jami’an soji sun bi sawunsu, lamarin da ya kai ga kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da adadin mutanen da suka kuɓuta ba, ko kuma inda waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwar suke.

Wannan hari ya zo ne makonni kaɗan bayan sace Ahmed Abubakar Zakka, matarsa da kuma ’yarsu mai watanni shida, Fatima, daga Alrahus Estate a ranar 6 ga Oktoba.

Lamarin ya ja hankalin jama’a sosai bayan bayyanar wani bidiyo da ya nuna iyalan suna hannun masu garkuwa da mutane, waɗanda rahotanni suka ce sun buƙaci a biya su kuɗin fansa har Naira miliyan 300 domin sakin su.

Sai dai iyalan sun samu ’yancinsu bayan shafe kwanaki tara a hannun masu garkuwar, lamarin da ya kawo farin ciki a tsakanin dangi da ’yan'uwa da sauran mazauna yankin. Daga bisani Gwamna Uba Sani ya ziyarce su.

Yawaitar irin waɗannan hare-hare ta ƙara ƙarfafa kiraye-kirayen neman ɗaukar matakan tsaro masu inganci, inganta sa ido da kuma ƙara kariya ga gidajen zama da sauran al’ummomin yankin.

Mazauna yankin sun kuma buƙaci a riƙa gudanar da sintiri akai-akai tare da tsaurara sa ido kan ƙofofin shiga da fita domin hana masu ɗauke da makamai samun damar shiga unguwannin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan sabon harin ba.

Sabon harin ya sake bayyana ƙalubalen tsaro da wasu sassan jihar Kaduna ke fuskanta, tare da nuna buƙatar ɗaukar matakan haɗin gwiwa cikin gaggawa domin kare rayukan jama’a da kuma daƙile sake faruwar irin waɗannan hare-hare masu tayar da hankali.

No comments