Rage Farashin Mai Na Kwana 30 Da Gwamnatin Tinubu Ta Yi, Siyasa Ko Tausayin Talakawa?
Daga Hadi Bawa
Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta yi na rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya, musamman kan dalilin da ya sa aka ɗauki matakin a daidai wannan lokaci da ya rage kwanaki 100 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Gwamnatin ta sanar da ɓullo da rangwame kan farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na kamfanin NNPC, na tsawon kwanaki 30, inda aka bai wa masu motocin sufuri na jama’a fifiko wajen cin gajiyar tsarin.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙin Ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai kan farashin fetur da batun tallafin man fetur a Abuja.
Sai dai Oyedele ya ce matakin ba yana nufin gwamnati ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba ne, illa dai rage farashin da NNPC ke sayar da man fetur da shi ga ’yan ƙasa, domin rage musu raɗaɗin hauhawar farashin mai.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na tattaunawa kan sanya iyakar farashin saukar da fetur daga matatar mai ko kuma farashin shigo da shi ƙasar nan a kan Naira 1,350 kan kowace lita, domin rage yawan sauye-sauyen farashin man fetur da ake samu a kai a kai.
Sai dai wasu masu nazarin harkokin siyasa na ganin matakin ba ya rasa nasaba da yanayin siyasar ƙasar da kuma alƙawuran da wasu ’yan adawa ke yi gabanin zaɓen 2027. Sun danganta hakan da alƙawarin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi na sake dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi.
A cewar masu wannan ra’ayi, matakin na Gwamnatin Tinubu na iya kasancewa wani yunƙuri na rage matsin lambar da ake fuskanta daga ’yan ƙasa, musamman ganin yadda batun farashin man fetur ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke jefa gwamnatin cikin suka tun bayan cire tallafin man fetur a 2023.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana ɗaukar wasu matakai domin rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin hauhawar farashin man fetur, ciki har da ƙara tallafin kuɗi ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi, bayar da rancen kuɗi mai sauƙi ga ƙananan ’yan kasuwa da masu amfani, da kuma hanzarta aiwatar da shirin samar da motocin da ke amfani da iskar gas (CNG).
Ministan ya jaddada cewa matakan da gwamnati ke ɗauka ba su nufin dawo da cikakken tallafin man fetur ba, yana mai cewa hakan zai iya haifar da matsalolin dogon lokaci domin magance matsalar gajeren lokaci.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da farashin fetur a gidajen man NNPC ke sauyawa daga jiha zuwa jiha. Sabon jadawalin farashin da NNPC ta fitar ya nuna cewa ana sayar da litar fetur kan Naira 1,355 a Legas da Rivers, yayin da Abuja ke kan Naira 1,370.
Sai dai wasu masu rajin kare haƙƙin talakawa, ciki har da Barista Abba Hikima, sun bayyana cewa abin da ’yan Najeriya ke buƙata shi ne rage farashin man fetur na dindindin, ba rangwamen da zai ɗauki kwanaki 30 kawai ba.
Wasu daga cikin masu sukar matakin na ganin cewa lokaci da yanayin da aka sanar da rangwamen na iya sanya wasu su fassara shi a matsayin wani matakin siyasa gabanin babban zaɓen 2027, yayin da masu goyon bayan gwamnati ke kallonsa a matsayin ƙoƙarin rage wa ’yan ƙasa wahalar da hauhawar farashin man fetur ta haifar.
A ƙarshe, babban abin da ke ci gaba da tayar da muhawara shi ne ko rangwamen na kwanaki 30 zai zama matakin gaggawa na rage wa talakawa nauyi ne kawai, ko kuma wata alama ce ta sauya salon gwamnatin Tinubu wajen tunkarar matsalar farashin man fetur da kuma tasirinsa ga rayuwar ’yan Najeriya.


No comments