Pantami da Gwarzo da Adebutu Suna Da Sauran Fata Bayan Sunayensu Sun Yi Ɓatan Dabo A Ƙumshiyar INEC
Daga Hadi Bawa
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta cire sunayen wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen ƙarshe na zaɓen 2027 da fitar ne saboda jam’iyyunsu sun gaza miƙa mata rajistar mambobinsu kamar yadda doka ta tanada.
Kamar yadda TNL HAUSA ta samu rahoto, wannan bayani na INEC ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun martani daga jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da abin ya shafa, bayan wallafa jerin sunayen ƙarshe da ba su ƙunshi wasu fitattun ’yan takara ba.
Daga cikinsu akwai ’yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihohin Gombe, Ogun da Kano, wato Isa Pantami da Ladi Adebutu da kuma na jam'iyyar NDC, Abdussalam Gwarzo.
An cire sunan Pantami ne bayan ya lashe zaɓen fidda gwani na PDP da kotu ta bayar da umarnin sake gudanarwa a jihar Gombe.
Haka kuma, ba a ga sunan Adebutu da na abokin takararsa a jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar Ogun ba.
Daga bisani, jam’iyyar PDP reshen Ogun ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da matsa wa INEC lamba, yayin da lauyan kare haƙƙin bil’adama, Inibehe Effiong, ya yi kira ga hukumar da ta tabbatar da cewa tana gudanar da ayyukanta ba tare da nuna son kai ba.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan INEC na ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu a ranar Talata, hukumar ta ce matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, a shari’ar INEC da Labour Party, mai lamba SC/CV/495/2026.
A cewar hukumar, Kotun Ƙolin ta tabbatar da cewa Sashe na 77(5) zuwa (7) na Dokar Zaɓe ta 2026 sun dace da Kundin Tsarin Mulki.
Waɗannan tanade-tanade sun wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu ga INEC cikin wa’adin da aka ƙayyade.
Kotun ta kuma tabbatar da jadawalin INEC da ya tanadi cewa jam’iyyun siyasa su miƙa rijistar mambobinsu tsakanin 21 ga Afrilu da 10 ga Mayu, 2026.
A cewar hukumar, Kotun Ƙolin ta yanke hukuncin cewa jam’iyyun siyasa da suka gaza bin waɗannan ƙa’idoji ba su cancanci tsayar da ’yan takara a zaɓen ba.
INEC ta ce ta yi amfani da wannan hukuncin ne wajen fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna, bisa tanadin Sashe na 287(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima
Hukumar ta kuma bayyana cewa ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 12 ga Satumba, 2026, wato kwanaki 13 kafin Kotun Ƙolin ta yanke hukuncin.
Ta ƙara da cewa, bisa Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, jam’iyyun siyasa da ke ganin an cire sunayen ’yan takararsu bisa kuskure suna da kwanaki 14 daga ranar wallafa jerin sunayen domin sanar da hukumar.
INEC ta sanya ranar 24 ga Oktoba, 2026, a matsayin wa’adin ƙarshe na miƙa irin waɗannan sanarwa.
Hukumar ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya, bin doka da oda, da kuma gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya.


No comments