Breaking News

NWAPDI A Zamfara : Tayi Kira Ga Gwamnati Ta samarwa Mata Manoma Da Cibiyar Rainon Irin Shuka



Daga Hussaini Yero, Funtua 

Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Aikin Noma (NWAPDI) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da ta baiwa manoman mata damar samun fili, dan ayyukan fadada ilimin noma da kuma kayayyakin noman zamani domin bunkasa noman abinci da karfafa wadatar abinci a cikin Jihar.

Ko'odinetar NWAPDI  Jihar, Hajiya Shafa'atu Habibu Tsafe, ta yi wannan kiran ne a yayin bikin Ranar Abinci ta Duniya na shekarar 2026 da kungiyar ta shirya a hedikwatar Ma'aikatar Noma da ke Gusau.

A cewarta, NWAPDI za ta tallafawa manoman mata 150 da kayayyakin noman iri-iri, da suka hada da taki, iri, maganin kwari, da kayan sarrafa amfanin gona, da sauransu, domin inganta harkokin nomansu.

Hajiya Shafa'atu ta roki Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara ,Huriyya Dauda da ta tallafawa kungiyar da cibiyar horarwa ga membobinta, da gidan gona na (Greenhouse ) domin renon tsirrai da kuma motocin da za su saukaka ayyukanta na noma a fadin jihar.

Ko'odinetar ta bayyana cewa, taken Ranar Abinci ta Duniya na 2026, "Kirkire-kirkire a Yau, don Ciyar da Gobe," ya nuna muhimmancin kirkire-kirkire masu amfani a fannin noma, musamman wadanda mata da matasa suka runguma don inganta noman abinci da adana albarkatun noman.

Ta bayyana amfani da bawon dankali da bawon doya wajen ciyar da awaki da sauran kananan dabbobi a matsayin wata hanya ta kirkire-kirkire ta rage sharar gona, yayin da take karfafa manoman dabbobi matasa su yi amfani da ma'auni don sanin ainihin nauyin dabbobinsu da kuma kaucewa yaudarar 'yan kasuwa.

Hajiya Shafa'atu ta kara jaddada cewa NWAPDI ta gabatar da shirye-shirye da dama don tallafawa manoman mata a Jihar Zamfara, ciki har da lambunan al'umma inda mata ke noman tumatir, kabeji, karas da dankalin Hausa a lokacin rani.

Ko'odinetar ta bayyana cewa, kungiyar ta kuma tallafawa mata 95 a fadin kananan hukumomi 14 na jihar ta hanyar raba kananan dabbobi.

Ta danganta raguwar mace-macen dabbobi daga kusan kashi 50 cikin 100 zuwa kasa da kashi 10 cikin 100 ga ingantattun ayyukan kula da lafiyar dabbobi, musamman rigakafi, ta jaddada bukatar rungumar hanyoyin kula da dabbobi da kimiyya ta tabbatar.

A bangaren abinci mai gina jiki, ta bayyana kokarin kungiyar na inganta cin abinci mai cike da sinadirai mai tauraro hudu ta hanyar karfafa gidaje su hada dankalin Hausa, madarar akuya, koren ganye da tumatir domin samar wa yara abinci mai gina jiki ta amfani da kayan amfanin gona da ake samu a cikin gida.

Ko'odinetar NWAPDI ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta samar wa manoman mata fili, inda ta ba da shawarar cewa, a ware akalla rabin eka ga rukunin mata 20, musamman a cikin al'ummomin da ke kusa da madatsun ruwa, domin tallafawa noman rani.

Ta kuma yi kira ga gwamnati da ta tura jami'an fadada ilimin noma domin jagorantar manoma kan ingantattun dabarun noma, kula da amfanin gona da kuma ayyukan noma masu dorewa.

Hajiya Shafa'atu ta karfafa manoman mata da su adana iri a kwalabe ta amfani da toka, su yi takin gargajiya daga kashin akuya kuma su ajiye akalla naira 500 a kowane mako ta hanyar Kungiyoyin Tattara Kudi da Bayar da Lamuni na Kauye (VSLAs) domin tallafawa ayyukan noma na gaba.

Ta shawarci matasa da su dauki noma a matsayin sana'a mai kawo riba, musamman ta hanyar kiwon dabbobi don kitawa, wanda ta bayyana a matsayin damar samun kudin shiga da kuma bayar da gudummawa ga wadatar abinci.

A jawabin ta Uwar Gidan Gwamnan Zamfara Hajiya Hurriya Dauda Lawal ta nuna gamsuwa da inganci da bambancin kayayyakin amfanin gona da manoman suka nuna, ta bayyana jajircewarsu, kwazonsu da kuma yawan amfanin da suke samarwa a matsayin abin karfafa gwiwa da alamun ci gaba a fannin noma na jihar.

Ta ce nunin ya nuna karuwar jajircewar mata ga noma da kuma muhimmiyar rawar da suke takawa wajen inganta rayuwar gidaje, da karfafa wadatar abinci da bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki.

 Hurriya ta lura cewa, ta halarci wani baje kolin noma makamancin wannan da Kungiyar Matan Manoma ta Najeriya (NAWIA) ta shirya kwanaki biyu da suka gabata, inda manoman mata ma suka nuna amfanin gonarsu.

Ta yaba wa Ko'odinetar NWAPDI ta Jihar, Hajiya Shafa'atu Habibu Tsafe, kan jajircewarta, kwazonta da kuma sadaukarwarta wajen tallafawa manoman mata da inganta ci gaban noma a Jihar Zamfara.

Uwargidan Gwamnan ta kuma yaba wa mijinta, Gwamna Dauda Lawal, kan sanya walwalar manoma a cikin abubuwan da gwamnatinsa ta ba fifiko, inda ta lura cewa, samar da tallafin noma, taki da sauran matakan tallafi na nuna kudirin gwamnati na inganta yawan amfanin gona.

Da take jawabi ga wadanda suka amfana, Hajiya Hurriya ta bukace su da su yi amfani da kayayyakin noman da aka raba a wajen taron cikin hikima domin inganta ayyukan nomansu, kara yawan amfanin gona da samar da kudin shiga mai kyau ga iyalansu.

A yayin taron, manoman mata sun nuna kayayyakin amfanin gona iri-iri, abinci da abin sha da aka shirya a cikin gida da sauran abubuwan dadi yayin da uwargidan Gwamnan ta zagaya rumfunan baje kolin don duba kayayyakin da aka nuna da kuma yaba kokarin manoman matan.

Ranar Abinci ta Duniya ana bikin ta ne a duk shekara a ranar 16 ga Oktoba domin wayar da kan jama'a game da yunwa, inganta wadatar abinci da kuma karfafa mataki don gina tsarin abinci mai dorewa.

No comments