Breaking News

Mun Sha Baƙar Azaba A Hannun Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mu -Ɗan NYSC

Daga Hadi Bawa

Ɗaya daga cikin matasa 20 masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da suka tsira baya an sace su a jihar Imo, ya bayyana yadda waɗanda suka yi garkuwa da su suka riƙa azabtar da su.

TNL HAUSA ta samu rahoton cewa, masu garkuwar sun riƙa ba su garin rogo da aka jiƙa da gurɓataccen ruwa a lokacin da suke tsare da su a cikin daji.

Matashin, wanda ya yi hira da BBC Pidgin ranar Litinin, ya ce masu garkuwar sun ba su damar kiran iyalansu, amma duk wanda maganganunsa suka fusata su, sai sun hukunta shi.

“An ba mu waya domin mu kira iyalanmu. Amma idan wani daga cikin iyalanmu ya faɗi abin da ba sa son ji, ko wani abu da zai fusata su, za a yi wa wannan mutumin duka. Har da amfani da bindiga wajen bugunsa,” in ji matashin.

Ya ƙara da cewa galibi maza ne masu garkuwar suka fi yi wa duka, yayin da suke nuna ɗan sassauci wajen dukan mata.

“Wani lokaci suna amfani da hannayensu wajen naushi, musamman maza. Amma ba su cika ɗaukar irin wannan matakin ba a kan mata,” in ji shi.

An sace matasan 20 da masu yi wa ƙasa hidima ne a ranar 1 ga Oktoba, yayin da suke tafiya daga Ibadan, jihar Oyo, don zuwa sansanonin horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin Abia da Akwa Ibom.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na safiya a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha, a yankin Umunoha da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, lokacin da wasu ’yan bindiga suka tare motocin bas guda biyu da ke ɗauke da matafiyan.

Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa na Naira miliyan 50 kan kowane mutum, kafin daga bisani su rage kuɗin.

Yayin da ake ci gaba da neman waɗanda aka sace, rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa jami’anta sun gano maɓoyar masu garkuwar ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuƙi (drones). 

Sai dai sun fuskanci matsala wajen isa wurin saboda zargin dasa abubuwan fashewa da aka kewayen sansanin.

An samu nasarar kuɓutar da matasan ne a ranar 7 ga Oktoba, bayan kwanaki bakwai da sace su, a wani aikin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro. Bayan an kuɓutar da su, an kai su asibiti domin duba lafiyarsu da ba su kulawa.

Da yake ba da labarin yadda tafiyar ta fara, matashin ya ce sun tashi ne da misalin ƙarfe 9 na safe, inda suka yi tsayawa a wurare daban-daban kafin su isa Onitsha. A nan ne direbansu ya sanar da su cewa za su kwana a wurin.

Ya ce tun da farko, fasinjojin sun roƙi direban da su ci gaba da tafiya tun lokacin da suka isa Ore, domin guje wa jinkiri a hanya.

No comments