Breaking News

Majalisar Dattawa Za Ta Ƙarfafa Ikon NUC Kan Jami’o’i Masu Zaman Kansu

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da karatun farko na biyu kan kudirin dokar da zai ƙarfafa ikon Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) wajen hukunta jami’o’in da suka karya ƙa’idojin gudanar da harkokin ilimi.

Kudirin na neman sauya dokar NUC domin bai wa hukumar ƙarin ikon sa ido, tabbatar da ingancin ilimi da kuma ɗaukar matakan ladabtarwa kan jami’o’in da suka aikata ba daidai ba.

A yayin muhawarar kudirin, an bayyana zarge-zargen karya ƙa’idoji da ake yi wa shugabancin Jami’ar Tansian da ke Umunya, a Jihar Anambra, lamarin da ya sa Majalisar Dattawan ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da jami’ar.

Fassara: Zainab Idris Bamalli
TNL HAUSA

No comments