Majalisar Dattawa Na Shirin Inganta Makarantun Sakandare
Majalisar Dattawan Najeriya na duba wani kudirin doka da ke neman ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi domin inganta makarantun sakandare na gwamnati, musamman wajen samar da kayan more rayuwa da na koyarwa.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa kudirin zai taimaka wajen inganta harkokin ilimi a ƙasar.
A wani rahoton kuma, Majalisar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan shawo kan matsalar zaizayar ƙasa a al’ummar Obogoro da ke Jihar Bayelsa, inda sama da mutum 300 suka rasa matsugunansu.
Daga: Zainab Idris Bamalli
TNL HAUSA


No comments