Breaking News

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Ya Yaba Wa Sarki Bayero Kan Mutunta Doka

Daga Hadi Bawa 

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa mutunta doka da kuma bin umarnin da hukumomin tsaro suka bayar.

TNL HAUSA ta ba da rahoton cewa, Bakori ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin a fadarsa da ke Nasarawa, Kano, bayan sarkin ya sanar da hukumomi cewa yana shirin hawa doki zuwa Yakasai a yau Alhamis, domin halartar bikin saukar karatun Alƙur’ani.

Kwamishinan ya ce dalilin ziyarar tasa shi ne roƙon sarkin da ya dakatar da shirin hawa dokin, domin kiyaye zaman lafiya da tsaron jama’a.

Ya bayyana cewa, bisa ƙa’idar hukumomin tsaro, duk wanda ke shirin hawa doki a bainar jama’a wajibi ne ya sanar da hukumomi a rubuce aƙalla sa’o’i 72 kafin lokacin taron. Sai dai duk da haka sai Kwamishinan ya roƙo sarkin da ya soke shirin nasa gaba ɗaya.

Bakori ya shawarci sarkin da ya je wajen taron da mota, kamar yadda ya saba yi a baya, yana mai cewa hukumomin tsaro na damuwa ne da hana duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar jama’a a Kano.

Kwamishinan ya bayyana Sarkin Bayero a matsayin basaraken gargajiya mai bin doka, wanda akai akai yake mutunta umarnin hukumomin tsaro tare da bai wa zaman lafiya muhimmanci.

Haka kuma, ya roƙi Alhaji Aminu Babba Ɗan’agundi, Sarkin Dawaki Babba da ya ci gaba da mara wa sarkin baya tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin masarautar da hukumomin tsaro.

A nasa jawabin, Sarkin Bayero ya gode wa kwamishinan da tawagarsa bisa ziyarar, inda ya tabbatar musu da cikakken haɗin kansa.

Sarkin ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankalin Kano na daga cikin abubuwan da ya fi ba muhimmanci, yana mai cewa zai ci gaba da tallafa wa duk wani ƙoƙari na tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda.

Wannan sa-in-sar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama a tsakanin gidajen sarautar Kano, wadda a baya ta haifar da takun saƙa bayan rikicin da aka yi a kusa da fadar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ke zaune.

A watan Disambar 2024, jami’an tsaro sun toshe ƙofar Gidan Rumfa, lamarin da ya taƙaita zirga-zirgar shiga da fita daga fadar tare da hana sarkin halartar wani bikin da aka shirya gudanarwa a Bichi.

Wasu masu sharhi kan harkokin tsaro a Kano sun bayyana tattaunawar da Bakori ya yi da Sarkin Bayero a matsayin wata hanya ta magance matsaloli ta hanyar tattaunawa, yayin da ake kare martabar masarautar gargajiya.

Sun ce ci gaba da tattaunawa kai tsaye da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma na iya taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano da magance matsalolin tsaro da ke ci jama'a tuwo a ƙwarya.

No comments