Houthi Sun Yi Ikirarin Kai Hari Kan Muhimman Wuraren Mai A Saudiyya
Daga: Hauwa’u Maikudi
Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta yi ikirarin kai hare-hare kan wasu muhimman wuraren jigilar ɗanyen mai a Saudiyya, lamarin da ka iya ƙara tayar da hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
A cewar rahoton da aka danganta ga kamfanin dillancin labarai na Reuters, kakakin sojin Houthi, Yahya Saree, ya bayyana cewa ƙungiyar ta kai hare-hare kan wasu wuraren mai da kuma filin jirgin saman King Khalid da ke Riyadh, babban birnin Saudiyya.
Rahoton ya ce Houthi ta yi zargin amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-haren.
Sai dai rundunar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ta bayyana cewa ta tare wani makami mai linzami da aka harba zuwa Riyadh, tare da lalata wasu na’urorin harba makamai masu linzami a birnin Sanaa na Yemen.
Ba a tabbatar da cikakken tasirin hare-haren da Houthi ta yi ikirarin kaiwa kan wuraren mai ba.
Bututun mai na East-West na daga cikin muhimman hanyoyin da Saudiyya ke amfani da su wajen jigilar ɗanyen mai daga gabashin ƙasar zuwa gabar Tekun Bahar Maliya domin fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.
Ana fargabar cewa duk wani hari da zai shafi samarwa ko jigilar mai a yankin na iya janyo sauye-sauye a kasuwar makamashi ta duniya.
TNL HAUSA


No comments