Breaking News

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Ƙarin Haske Kan Hatsarin Da Jirgin Sojan Sama Ya Yi A Ondo

Daga Aliyu Saleh 

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya Festus Keyamo, ya ce mutane 32 ne cikin jirgin saman soja da ya yi yau a Litinin a Igbokoda, Jihar Ondo.

Keyamo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce jimillar mutane 32 da ke cikin jirgin 25 sojoji ne, yayin da bakwai kuma ma'aikatan jirgin a daidai lokacin da hatsarin ya afku.

Ya ce masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun sanar da ɓacewar jirgin sojin mai lamba NGR 931, wanda ke kan hanyarsa daga Benin zuwa Lagos.

A cewarsa, jirgin ya ɓace daga na’urar radar da misalin ƙarfe 9:13 na safe, bayan duk ƙoƙarin da aka yi na samun sadarwar rediyo da ma’aikatan jirgin ya ci tura.

Keyamo ya ce daga baya aka tabbatar da cewa jirgin ya yi hadari a kusa da sansanin sojojin ruwa da ke Igbokoda, inda aka gano tarkacen jirgin, yayin da ake ci gaba da ayyukan ceto da neman waɗanda ke cikin jirgin.

Ministan ya ce ya tuntuɓi Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan Ma’aikatar Jiragen Sama wajen gudanar da aikin ceton. 

Ya ƙara da cewa za a fitar da ƙarin bayani kan lamarin nan gaba.

Wata majiya ta shaida wa TNL HAUSA cewa, an jirkinta fitar da sunaye da adadin waɗanda suka rasu ne domin a fara sanar da iyalansu.

No comments