Breaking News

Gwamnatin Tinubu Ta Sake Jefa 'Yan Najeriya Cikin Talauci -NDC


Daga Hadi Bawa

Jam’iyyar NDC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙara tsananta halin ƙunci da talauci da 'yan Najeriya ke fuskanta. 

NDC ta yi ishara ga ƙarin kuɗaɗen shiga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ba'a shekarar 2026/2027, inda ɗaliban Najeriya masu karatun digiri za su biya tsakanin N143,000 zuwa N298,000, gwargwadon fannin karatu da matakin ɗalibi.

TNL HAUSA ta ba da rahoton cewa a baya ɗalibai na biyan tsakanin N62,000 zuwa N84,000 a ƙarƙashin tsohon tsarin.

Da take martani kan ƙarin kuɗaɗen, NDC ta ce matakin zai ƙara wa iyalan ma’aikata nauyi, musamman waɗanda ke fama da matsalar tattalin arziƙi wajen ɗaukar nauyin karatun ’ya’yansu a jami’o’i.

Jam’iyyar ta ce iyaye da dama ba sa iya biyan kuɗin karatun manyan makarantu a halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki. 

NDC ta ce albashin da yawancin ma’aikatan da suka dogara da jami’o’in gwamnatin tarayya kamar ABU ke samu “ba ya kai su ƙarshen wata, balle ya iya ɗaukar nauyin wannan ƙarin kuɗin makaranta.”

NDC ta bayyana ƙarin kuɗaɗen a matsayin wani ƙarin nauyi ga ɗalibai da iyalansu, tana mai ɗora alhakin abin da ta kira “manufofin da ba su fifita talakawa ba” na gwamnatin Tinubu kan ƙara tsanantar talauci ga jama'ar ƙasar nan.

Jam’iyyar ta kuma nuna tausayinta ga ɗaliban ABU da abin ya shafa, tana mai cewa suna fuskantar sakamakon manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu.

NDC ta yi alƙawarin cewa idan aka kafa gwamnatin da Peter Obi zai jagoranta, za ta bai wa jami’o’i tallafin da ya dace, tare da samar da yanayin da zai ba matasan Najeriya damar samun ilimi cikin kwanciyar hankali da lumana.

No comments