Breaking News

Gombe: In Ka Shirya Ka Zo Mu Baje Manufofinmu A Fili – Ɗan Takarar NDC Ya Ƙalubalanci Pantami

 

Daga Idris Khalid

Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sadiq Abubakar, ya ƙalubalanci ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, da ya fito su fafata muhawarar siyasa ta bainar jama’a gabanin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.

A cewarsa, ta hanyar muhawarar al'ummar jihar Gombe za su fahimci wanene ke da kyakkyawar manufofi da tsare-tsaren da za su ciyar da jihar gaba a tsakanin shi da Pantami.

Abubakar ya yi wannan ƙalubalen ne cikin wata sanarwa da ya fitar ’yan jarida jiya, inda ya ce muhawarar za ta bai wa ’yan siyasar biyu damar gabatar da manufofinsu, tsare-tsarensu da kuma hangen nesansu kan ci gaban jihar Gombe.

Ya ce irin wannan muhawara za ta bai wa al’ummar jihar damar tantance fahimtar ’yan takarar game da shugabanci da kuma abubuwan da suka sanya a gaba wajen tsara manufofi, maimakon dogaro kacokan da kalaman yaƙin neman zaɓe.

A cewarsa, muhawarar za ta kuma bai wa al’ummar Gombe damar ji kai tsaye daga bakin ’yan takarar kan matsalolin da ke addabar al’ummominsu da kuma matakan da suke shirin ɗauka idan aka zaɓe su.

Abubakar ya ce muhawarar siyasa na daga cikin muhimman ginshikan dimokuradiyya, domin tana bai wa ’yan takara damar tattauna batutuwan da suka shafi al’umma, tare da bai wa masu kada kuri’a damar nazarin shirye-shiryensu da hanyoyin da suke son bi wajen magance matsalolin jama’a.

Saboda haka, ya yi kira ga Pantami da ya amince da ƙalubalen tare da shiga cikin muhawarar da za ta mayar da hankali kan ci gaba da walwalar al’ummar jihar Gombe.

Ɗan takarar NDC ya ce ya kamata muhawarar ta mayar da hankali kan batutuwan shugabanci, bunƙasar tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, tsaro da samar da ayyukan yi.

Ya ƙara da cewa, muhawarar bai kamata ta karkata zuwa ga son zuciya ko muradun jam’iyya ba, sai dai ta sanya makomar jihar Gombe a matsayin muhimmin batu a tsakiyar tattaunawar siyasa.

Abubakar, wanda ya taɓa riƙe mukamin Shugaban Matasa na Kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya fice daga jam’iyyar zuwa NDC a shekarar 2026, inda daga bisani ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar a zaɓen 2027.

No comments