Breaking News

Fati Muhammad Ta Samu Muƙami a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Abba Kabir Yusuf

Daga Hadi Bawa 

Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Fati Muhammad, ta bayyana godiyarta ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa naɗa ta a matsayin Mataimakiyar Darakta  mai kula da mata a ɓangaren nishaɗi a kwamitin yaƙin neman zaɓensa karo na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

TNL HAUSA ta jiwo cewa Fati Muhammad ta bayyana ta karɓi wannan naɗi cikin farin ciki da godiya, tana mai cewa matsay in da aka ba ta ba dama ce kawai ba, har ma amana ce da ke buƙatar jajircewa da ƙwazo wajen sauke nauyin da ke tattare da shi.

Jarumar, wacce ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce tana matuƙar godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan girmamawa da ya yi mata, tare da alƙawarin yin amfani da damar wajen bayar da gudunmawa ta gaskiya da aiki tuƙuru.
Ta kuma bayyana aniyarta ta yin aiki ba kama hannun yaro domin ganin ta sauke nauyin da aka ɗora mata yadda ya kamata, tare da haɗin gwiwar sauran mambobin kwamitin.

Fati Muhammad ta roƙi Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu, Ya kuma sanya ayyukan da za su gudanar su zama sanadin nasara da ci gaba.

Ta ƙara da cewa, yanzu an fara aiki, kuma za su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora musu.

A ƙarshe, jarumar ta sake miƙa godiyarta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amana da girmamawar da ya nuna mata, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa ɗaukaka da nasara.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yana neman zarcewa karo na biyu a jam'iyyar APC bayan ya sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP, tare da raba gari da ubangidansa Rabi'u Musa Kwankwaso.

No comments