DA DUMI-DUMI: 'Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Masussuka
Rahotanni daga Dutsinmar Jihar Katsina sun ce, wasu 'yan bindiga sun kashe fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheìkh Yahaya Ibrahim Masussuka, a gidansa dake Dutsimma.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe Tara na dare a ƙofar gidan malamin, inda maharan suka buɗe masa wuta tare da wani amininsa.
An dai garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Wakiliyarmu ta ce, babu wani ƙarin bayani kan waɗanda suka aikata kisan ko kuma dalilin kai harin.
Lamarin ya Æ™ara jefa al’ummar yankin cikin alhini, musamman mabiyan malamin da waÉ—anda suka san shi.


No comments