Breaking News

Ba Sauran Rikici Tsakanin Barau da Bichi -Gwamna Abba

Daga Ibrahim Muhammad 

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta tsakanin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, bayan takun saƙar siyasa da ya shiga tsakaninsu.

TNL HAUSA ta ruwaito cewa, an gudanar da taron sulhun ne a Abuja a Larabar nan, inda aka shafe kusan sa’o’i biyu ana tattauna batutuwan da suka shafi rashin jituwar da kuma makomar jam’iyyar APC a Kano.

Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai bayan tattaunawar.

A yayin taron, Gwamna Abba Yusuf ya buƙaci Sanata Barau da Hon. Bichi, tare da magoya bayansu da su ajiye duk wani bambanci da ke tsakaninsu, su mayar da hankali kan haɗin kan jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.

Gwamnan ya jaddada cewa samun nasarar APC a matakai daban-daban na buƙatar haɗin kai, fahimtar juna da jajircewar shugabanni da mambobin jam’iyyar.

Ya kuma yi kira ga magoya bayan ɓangarorin biyu da su guji kalaman ɓatanci, cin mutuncin juna da duk wani mataki da ka iya ƙara raba kan mambobin jam’iyyar.

Gwamna Abba ya ce haɗin kan shugabannin APC da magoya bayansu zai taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar da kuma tabbatar da haɗin kai a tsakanin mambobinta gabanin zaɓen 2027.

No comments