Breaking News

ASUU Ta Buƙaci Cire Sunan Shugaban Reshen UMYU Daga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC A Katsina

Daga Hauwa’u Maikudi

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), shiyyar Sokoto, ta buƙaci a cire sunan Farfesa Aminu Usman, shugaban reshen ƙungiyar na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU), daga jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a jihar Katsina.

A cewar wata sanarwa da mai kula da shiyyar Sokoto ta ASUU, Farfesa Abubakar Sabo, ya sanya wa hannu, Farfesa Usman bai amince da saka sunansa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko ba.

Sanarwar ta bayyana cewa sunan Farfesan ya bayyana a lamba ta shida a ƙarƙashin Daraktan Tsare-Tsare da Dabarun Yaƙin Neman Zaɓen. Ta ƙara da cewa ya riga ya rubuta wa Darakta-Janar na kwamitin wasiƙa yana neman a cire sunansa.

ASUU ta buƙaci masu shirya kwamitin su mutunta wannan buƙata, tare da jan hankalin jama’a da kada su ɗauki saka sunan a matsayin hujjar cewa Farfesa Usman yana goyon bayan yaƙin neman zaɓen ko manufofinsa.

Ƙungiyar ta jaddada cewa ASUU ƙungiya ce mai zaman kanta wadda ba ta goyon bayan wata jam’iyyar siyasa. Sai dai ta amince cewa mambobinta suna da ƴancin zaɓen jam’iyyar da suke so da shiga harkokin siyasa bisa tanadin doka.

A cewar sanarwar, ya kamata shugabannin ƙungiyar su bambanta ra’ayoyinsu na siyasa da nauyin da ke kansu na kare martaba da ’yancin cin gashin kan ASUU.

Shiyyar Sokoto ta kuma buƙaci duk wani shugaban reshen ASUU na UMYU da aka saka sunansa a jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen ba tare da izininsa ba, da ya nemi a cire sunan, tare da bayyana matsayinsa idan hakan ya zama dole.

ASUU ta ƙara da cewa duk wani matakin siyasa da shugaban ƙungiyar ya ɗauka wanda ya saɓa wa ƙa’idojinta, ya kamata a magance shi bisa tanadin dokoki da hanyoyin ladabtarwa na ƙungiyar.

Ƙungiyar ta bayyana cewa matsayarta ba ta shafi APC ko wata jam’iyyar siyasa kai tsaye ba. A maimakon haka, manufarta ita ce kare ƴancin cin gashin kan ASUU, haɗin kan mambobinta da muradun malaman jami’o’i.

No comments