Ana Juyayin Mutuwar Tsohon Gwamnan Delta
Daga Hadi Bawa
Tsohon gwamnan jihar Delta, Dakta Emmanuel Eweta Uduaghan, ya rasu yana da shekaru 71 a duniya bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Iyalansa ne suka sanar da rasuwar tasa a cikin wata sanarwa da Toju Andre Uduaghan ya sanya wa hannu ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar, mai taken “Sanarwar Rasuwar Mai Girma Dakta Cif Emmanuel Eweta Uduaghan”, ta bayyana cewa rasuwar tsohon gwamnan babban rashi ne ga iyalansa, jihar Delta da ma Najeriya baki ɗaya.
A cewar sanarwar, marigayin ya rasu ne a safiyar ranar 19 ga Oktoba, 2026, inda iyalansa suka bayyana alhininsu kan rasuwar mutumin da suka ce ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu, tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma a jihar Delta da Najeriya.
Iyalansa sun bayyana shi a matsayin uba, ɗan’uwa, kawu kuma ginshiƙin ƙarfafa zumunci, inda suka ce za su yi matuƙar kewar rashin kasancewarsa a cikinsu.
Kafin zama gwamna, Uduaghan ya riƙe muƙamin kwamishinan lafiya daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan ya zama sakataren gwamnatin jihar Delta daga 2003 zuwa 2007. Daga nan ne ya zama gwamnan jihar, inda ya yi mulki daga shekarar 2007 zuwa 2015.
A lokacin da yake kan muƙaman gwamnati, ya bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ayyukan jin daɗin jama’a da samar da ababen more rayuwa a jihar Delta, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Iyalansa sun yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya ba shi hutu na har abada, sannan Ya ba iyalansa, abokansa da sauran waɗanda rasuwar ta shafa haƙurin jure wannan babban rashi.


No comments