Amurka Za Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Ga Tsohon Sojanta Kai-tsaye
Daga Zainab Idris Bam Alli
Gwamnatin Amurka na shirin zartar da hukuncin kisa ga Nidal Hasan, tsohon likitan tabin hankali a rundunar sojin ƙasar, wanda aka samu da laifin kashe sojoji 13 a wani harin da ya faru a sansanin soji na Fort Hood, da ke jihar Texas, a shekarar 2009.
TNL HAUSA ta ce an tsara zartar da hukuncin ne a ranar 3 ga Disamba, 2026, ta hanyar harbin bindiga daga ƙungiyar sojoji, kamar yadda bayanin ya nuna.
An danganta sanarwar shirin da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, wanda aka ce ya bayyana cewa manufar hukuncin a bainar jama'a hskan nanuna wa al'umma irin mummunan sakamakon da ke tattare da aikata manyan laifuffuka.
Wakiliyar TNL HAUSA ta nuna cewa Nidal Hasan, wanda ya kasance likitan tabin hankali a rundunar sojin Amurka, ya kai harin ne a ranar 5 ga Nuwamba, 2009, a wani ginin kula da lafiya da ke sansanin Fort Hood. Harin ya yi sanadin mutuwar sojoji 13, tare da jikkata wasu da dama.
A shekarar 2013, an gurfanar da Hasan a gaban kotun soji, inda ya amince da aikata harin. A lokacin, ya bayyana dalilan da suka sa ya aikata hakan, ciki har da abin da ya danganta da kare Musulmi da Taliban a Afghanistan.


No comments