Breaking News

2027: Shinkafi Dan Takarar Gwamnan Zamfara A ADC Ya Kaddamar Da Yakin Neman Zabensa Ya Kalubalanci Gwamnatin APC


Daga Hussaini Yero, Gusau 

Dan takarar gwamna A  Jam'iyyar ADC Hon Bilyaminu Yusuf Shinkafi, ya kaddamar da yakin kamfen dinsa da na 'Yan Majalisar Dattawa Da Wakilai da "Yan Majalisar Dokokin Jihar. Kuma ya Kalubalancin Gwamnatin APC Karkashin Jagorancin gwamna Dauda Lawal akan ayyukan da yace Yayiwa Kananan Hukumomi na naira biyan Ashirin da hudo A fadin jihar.

 Shinkafi ya bayyana haka ne alokacin kaddamar da yakin neman zabensa na gwamna a Gusau, babban birnin jihar, inda ya yi jawabi ga taron magoya bayan Jamiyyar ADC.

Dan Takarar Gwamnan ya bayyana cewa,babu inda Akai aikin da ya kai naira biyan Ashirin da hudo a mafiyawan Kananan Hukumomin.Inji Bilya Shinkafi .

Dan haka ya daukin alwashin idan al'ummar Jihar Zamfara suka zabe shi a zaben 2027 a matsayin gwamnan Jihar Zamfara,zayyi ayyukan cigaban al'umma a fadin Jihar ta Zamfara.

 A jawabin sa ya tabbatar da inganta tsaro, farfado da Ayyukan Noma, karfafa matasa da mata, da kuma fadada kasuwanci a fadin jihar.

Tsaro ya kasance wani lamari mai matukar muhimmanci a Zamfara, inda rashin tsaro ya kawo cikas ga hanyoyi, rayuwa, samar da kayan Gona, Kasuwanci, da rayuwar yau da kullum.

 Game da ci gaban tattalin arziki, dan takarar na ADC ya yi alkawarin bunkasa  Kasuwanci a matakai daban-daban, da  samar da damammaki ga mata da matasa don shiga cikin tattalin arzikin jihar yadda ya kamata.

No comments