2027: PDP Ta Yi Tir Da Cire Sunan Adebutu Daga Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Ogun
Daga Hadi Bawa
Jam’iyyar PDP a jihar Ogun ta yi kakkausar suka kan cire sunan ɗan takararta, Oladipupo Adebutu, daga jerin sunayen ’yan takarar da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
TNL HAUSA ta ba da rahoton cewa an wayi gari ba a ga sunan Adebutu daga cikin jerin sunayen 'yan takarar gwamnonin da INEC ta fitar ba kamar yadda sakatarenta, Rose Oriaran-Anthony ta bayyana ranar Asabar a Abuja.
Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta rahoton nan hukumar ba ta bayyana dalilin cire sunan nasa ba a cikin jerin 'yan takarar ba.
INEC ta amince da ’yan takara da mataimakansu daga jam’iyyu 13, ciki har da Olamilekan Adeola na jam’iyyar APC da Lawal Adebisi na jam’iyyar ADC.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulki a jihar Ogun da matsa wa INEC lamba domin hana ɗan takararta shiga zaɓen, saboda tsoron kayen da za ta iya sha.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Mista Adebayo, ya ce an cire sunan ɗan takararsu ne sakamakon matsin lambar da APC ta yi wa INEC saboda fargabar rasa zaɓen ga PDP.
Ya bayyana cewa Mista Adebutu bai taɓa barin PDP ba, kuma ya yi rajistar zama ɗan jam’iyyar a lokacin da aka tsara domin yin rajistar ta intanet, yana mai cewa yana da katin shaidar kasancewarsa ɗan jam’iyyar, an tantance shi, sannan aka miƙa bayanansa ga INEC a kan lokaci.
Mai magana da yawun PDP ya buƙaci al’ummar jihar Ogun da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa sunan ɗan takararsu, Hon. Oladipupo Adebutu, zai fito a jerin sunayen ’yan takarar, kuma zai zama gwamnan jihar Ogun.


No comments