2027: Gwamnan Kano Ya Buƙaci Jama’a Su Guji Abubuwan Da Za Su Kawo Tsaiko Ga Zaman Lafiya
Daga Hadi Bawa
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga al’ummar jihar da su guji duk wani aiki ko hali da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya, wanda aka gudanar a filin wasanni na cikin gida na Sani Abacha da ke Kano jiya Alhamis.
Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da rungumar zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna domin samar da yanayi mai kyau na bunƙasar tattalin arziƙi da ci gaban jihar.
“Yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, ina kira a gare ku da ku ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna. Mu guji tashin hankali da duk wani abu da zai iya barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin jiharmu,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma buƙaci al’ummar Kano da ’yan Najeriya baki ɗaya da su ci gaba da addu’ar Allah ya sa zaɓe cikin aminci da zaman lafiya, ’yanci, adalci da gaskiya.
Ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai kira ga jama’a da su guji tashin hankali, rarrabuwar kai, rashin haƙuri da aikata laifuka.
Ya ce gwamnatinsa na nan daram wajen ƙarfafa nasarorin da aka samu a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa, samar da ruwa, tsaro da bunƙasa jarin ɗan Adam.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya, ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya da shugabannin addini, ’yan kasuwa da hukumomin raya ƙasa domin yi wa al’ummar jihar hidima.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, tare da samar musu da ƙarin kayan aiki da tallafin gudanar da ayyuka, musamman sojoji, ’yan sanda, Hukumar Tsaron Fararen Hula da DSS, domin ƙarfafa tsaro a yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro.
Ya ce gwamnatinsa ta kuma ƙara mayar da hankali kan daidaita harkokin tsaro a matakin jiha, musamman a ƙananan hukumomin Tsanyawa, Ghari, Gwarzo, Shanono, Bagwai, Rogo, Kiru/Bebeji, Karaye da Tudun Wada/Doguwa, da sauran al’ummomin da ke fuskantar matsalolin tsaro, domin kare rayuka, dawo da amincewa juna da ba su damar komawa gonakinsu da harkokin tattalin arziƙi.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin tunkarar matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar su ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomi kan Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi da Safarar Su Ba Bisa Ƙa’ida Ba, tare da fitar da doka domin ƙarfafa yaƙi da miyagun ƙwayoyi, daba da sauran laifuka.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samar da jari na fara kiwon dabbobi, sana’o’i da sauran nau’o’in tallafi ga dubban mutane a faɗin jihar, a matsayin wani mataki na tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa tallafin da take bai wa jihar Kano wajen samar da muhimman ababen more rayuwa, tsaro da sauran shirye-shiryen ci gaba.


No comments