'Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan'wansa Saboda Abinci
Daga Hadi Bawa
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama wani mutum mai shekaru 37, Anthony Kosisochukwu Okafor, bisa zargin kashe ɗan'uwansa, Emmanuel Okafor, mai shekaru 45, sakamakon wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsu kan kayan abinci.
TNL HAUSA ta gani cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Adegbe, Abagana, ƙaramar hukumar Njikoka ta jihar Anambra.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar cewa, sun kama Kosisochukwu da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar 7 ga Fabrairun 2025, bayan faruwar lamarin.
Rundunar ta ce rikicin ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda ake zargin Kosisochukwu ya yi amfani da sanda wajen sheme Emmanuel a ƙirji.
Bayan faruwar hakan, an garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibiti domin samun kulawa, amma likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da cewa ya rasu.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, inda ya bayyana cewa gardamar da ta kai ga faɗan ta samo asali ne daga rashin jituwa kan amfani da kayan abincin da ke cikin gidan.
Rundunar ta ce lamarin ya jawo hankalin jama’a kan buƙatar magance rikice-rikicen cikin gida da kuma taƙaddama tsakanin ’yan'uwa cikin lumana domin kauce wa mummunan sakamako, amma haƙa ba ta cimma ruwa ba.
Bayan kama shi, an mayar da binciken lamarin zuwa Sashen Binciken Kisan Kai na Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Jihar, da ke Awka, domin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin kisan. Rundunar ta ce za a gurfanar da Kosisochukwu a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
’Yan sanda sun kuma jaddada muhimmancin koyon yadda ake sarrafa fushi da bambance-bambancen ra’ayi cikin hikima, musamman tsakanin ’yan'uwa da sauran waɗanda ke rayuwa tare.
A cewarsu, kyakkyawan tsarin warware rikici cikin hikima da kuma guje wa tashin hankali na da muhimmanci wajen hana irin waɗannan abubuwan da kan haifar da asarar rai da kuma sakamakon da ba za a iya gyarawa ba.


No comments