Breaking News

Yadda Rubuta 'Abba Must Go' Ta Ci Kujerar King Indara

Daga Hadi Bawa 

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya sallami ɗaya daga cikin hadimansa, Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara, sakamakon wasu rubuce-rubucen da ya wallafa a kafafen sada zumunta da suka shafi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka wa Sanata Barau kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Shitu Madaki Kunchi, ya fitar a ranar 18 ga Satumba, 2026, ta ce an cire Umar Alhassan daga muƙaminsa na Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kan Harkokin Majalisa (SLA).

A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan wasu rubuce-rubucen da King Indara ya wallafa a shafinsa na Facebook, ciki har da taken “Abba Must Go”, wanda ofishin Sanata Barau ya bayyana a matsayin rashin ɗa’a da rashin ladabi ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sanarwar ta ce irin wannan hali ya saɓa wa ƙa’idojin ladabi da mutunta muƙaman gwamnati da ake buƙata daga jami’an da ke aiki a ƙarƙashin ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ana sa ran masu riƙe da muƙaman siyasa za su kiyaye ɗa’a tare da ƙarfafa tattaunawa mai ma’ana tsakanin matakan gwamnati.

Ofishin Sanata Barau ya kuma bayyana cewa rubuce-rubucen sun saɓa wa ƙa’idojin jam’iyyar APC, inda Sanatan ya sake jaddada goyon bayansa ga jam’iyyar daga matakin ƙasa har zuwa matakin ƙananan hukumomi. Sallamar King Indara ta fara aiki ne daga ranar 18 ga Satumba, 2026.

Lamarin ya kuma sake fito da wata muhimmiyar fuska ta siyasar Kano, musamman dangantakar da ke tsakanin mabiyan tsohon Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran ɓangarorin siyasar jihar. 

Rahotanni sun ce bayan matakin sallamar, King Indara ya wallafa cewa “Kano is for Kwankwaso”, tare da bayyana cewa har yanzu shi ɗan jam’iyyar APC ne, amma ya nuna rashin goyon bayansa ga ci gaba da mulkin Gwamna Abba Yusuf.

Matakin ya zo ne a lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen 2027, yayin da ake samun bambance-bambancen ra’ayi tsakanin ’yan siyasa da magoya bayansu a Kano. 

Sai dai sanarwar ofishin Sanata Barau ta mayar da hankali ne kan abin da ta kira rashin ɗa’a, rashin ladabi da saɓa wa ƙa’idojin APC, ba tare da bayar da ƙarin bayani kan wata takamaiman taƙaddamar siyasa tsakanin Sanatan da Gwamnan Kano ba.

No comments