Breaking News

Ya Kamata Duk ’Yan Najeriya Su Samu Horon Aikin Soja -Ministan Tsaro

Daga Aliyu Saleh 

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ba da shawarar cewa ya kamata dukkan ’yan Najeriya su samu horon aikin soja domin su fahimci irin ƙalubalen da jami’an tsaron ƙasar ke fuskanta wajen kare ƙasa.

Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Ken Giami a shirin African Leadership Podcast. 

Ya ce horon soja, wanda ya ƙunshi jure yunwa, gajiya da wahalar motsa jiki, na iya bai wa mutum fahimtar rayuwa da nauyin da ke tattare da kare ƙasa ta wata hanya da ba za a samu irinta a wani wuri ba.

A cewarsa, idan talakawan ƙasa suka samu damar yin irin wannan horo, hakan zai taimaka musu wajen fahimtar aikin da jami’an Rundunar Sojin Najeriya ke yi da kuma irin sadaukarwar da suke yi domin kare ƙasa. 

Ya ce irin wannan gogewa za ta sauya fahimtar ’yan ƙasa game da rayuwa da nauyin da ke kansu na kare ƙasarsu.

Tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaro ya ce horon zai koya wa mutum yadda zai ci gaba da tafiya ko da yana cikin tsananin gajiya, yunwa ko rashin jin daɗin rayuwa. 

Ya ce mutum na iya yin tafiya ta tsawon kilomita, ya gaji matuƙa, amma duk da haka ya ci gaba saboda manufar da yake yi wa hidima.

Janar Musa ya ce: “Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya samu damar yin horon soja. Zan iya tabbatar muku cewa hakan zai ba ku wata fahimta ta daban game da rayuwa. Za ku fahimci abin da ake nufi da zama cikin yunwa da yin kwanaki ba tare da barci ba da kuma jure gajiya.”

Ya ƙara da cewa jami’an soja suna sadaukar da rayuwarsu ne domin kare ƙasa, yana mai danganta hakan da koyarwar Littafi Mai Tsarki da ke cewa babu abota mafi girma da ta wuce mutum ya sadaukar da ransa domin abokinsa. 

Ya ce saboda haka ne yake ganin bai dace a raina aikin soja ko a ce ba a buƙatar su ba, domin jami’an tsaron ƙasar na sanya rayukansu cikin haɗari domin kare sauran ’yan ƙasa.

No comments